Tawagar kwallon kafa ta Amurka ta soke ganawa da manema labarai
da aka shirya yi ranar Laraba, yayin da Manchester United ke shirin yunƙurin
ɗaukar babban kocinsu, Mauricio Pochettino. Press Association ta fahimci cewa an riga an samar da tsarin
da zai bai wa ɗan ƙasar Argentina damar komawa United idan aka sallami babban
kocin yanzu, Michael Carrick na fuskantar kalubale bayan da kungiyar ke yankin faɗuwa daga gasar, saboda mummunan sakamako a karon farko tun bayan 1986. An fahimci cewa Pochettino, wanda aka dauki hotonsa yana
jagorantar atisayen tawagar Amurka kamar yadda aka tsara a yammacin Laraba,
yana sha’awar karbar aikin Old Trafford, wanda aka yi ta danganta sunansa da
mukamin a lokutan baya. Pochettino tsohon kocin Tottenham da Paris St Germain da Chelsea ya sanya hannu kan sabon kwantiragin wata uku da suka
gabata domin ci gaba da zama kocin Amurka har zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2030,
kuma US Soccer za a biyata diyya idan ya amince da komawa Manchester
United. PA ta fahimci cewa US Soccer ta riga ta shirya yiwuwar
tafiyar Pochettino kuma tana da tsarin maye gurbinsa idan hakan ya tabbata. Tun farko an tsara cewar Pochettino zai gana da manema labarai kan wasan da Amurka za ta kara da Nations League zagayen kwata fainals da Haiti. Duk da jita-jitar da ke kewaye da Carrick, ya je atisaye a United kamar yadda ya saba a cibiyar horaswa ta United da ke Carrington a
safiyar Laraba. Ya bar Carrington da yammacin ranar Laraba ba tare da an
sanar da wani hukunci kan makomarsa ba. An tattauna matsayinsa a wani taro a
Monaco da babban jami’in gudanarwa Omar Berrada da daraktan kwallon kafa Jason
Wilcox suka yi tare da shugaba, Sir Jim Ratcliffe ranar Laraba.




